We know why we tour as tourists. |
Mun san dalilin dake sawa muke fita yawon bude ido. |
You know why you may choose some parts of the globe over others by reasons such as family, cheap prices and activities- but do you specifically know why we tour? |
Kasan dalilin da yasa kake zabar wasu bangarori na duniya fiye da wasu bangarorin; kamar iyali, saukin kudi, da kuma ayyukan gabatarwa. Amma ka san ainahin dalilin dake sawa muje yawon shakatawa? |
Tourism varies a number of ways: time, number of tourists, and different reasons being just some. |
Yawon bude ido ya rabu ta hanyoyi da dama; lokachin yinsa, yawan mutanen dake fita yinsa, da kuma wasu dalilai mabanbanta. |
For example, you may spend 2 weeks in Borth which has thousands of tourists, or you may tour in the Amazon for a month where there are little tourists and for the purpose of ecotourism. |
Ga misali zaka iya zuwa Borth na tsawon sati biyu gurin da yake da dubban masu yawon shakatawa, ko kuma ka ziyarchi Amazon har tsawon wata daya gurin da yake da karanchin masu yawon shakatawa da kuma rashin guraren ziyara masu yawa. |
Because of recent falls in the economy and general decrease of salary, many people are looking for cheaper places to tour. |
sakamakon matsalar tattalin arziki da kuma karanchin kudin albashi, mutane da dama suna neman gurin da yake da araha domin zuwa yawon shakatawa. |
This means more money for the cheaper resorts, that tend to be Mass Tourism destinations and a big company. |
Domin haka gurare masu sauki zasu fi samun kudin shiga mai yawa, sakamakon ziyarar dumbin al-umma. |
Tourism can have positive and negative effects: money, jobs and a good recognition are common positives that tourism brings. |
Yawon bude ido yana da tasiri mai kyau da kuma akasin haka; kudi, aikin yi, da sanayya na daga cikin abubuwa masu kyau da yawon shakatawa ke haifarwa. |
However, Global warming, pollution and destruction of habitat are all negatives people are concerned about. |
Sai dai kuma dumamar yanayi, gurbata da lalata muhalli wadanda ke faruwa a sakamakon yawon bude ido sune abubuwan da suka fi damun mutane. |
Solutions are being carried out to make tourism more eco-friendly. |
Ana kokarin samar da mafita domin kawar da matsalolin yawon bude ido game da muhalli. |
Eco-tourism helps local communities, wildlife and produces much less pollution than mass tourism. |
Yawon bude ido mara illa, yana taimakawa al'umma da namun daji, yana kuma da karanchin kawo gurbatar muhalli. |
But are the general public willing to tour in eco-tourist destinations? |
Sai dai abin tambaya shine shin al'umma nada ra'ayin gudanar da yawon bude ido a guraren da suka fi dacewa? |